ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Tahsin Alkhaffaji kakakin rundunar hadin guiwar yana fadawa kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki a safiyar yau Litinin.
Alkhaffaji ya bayyana cewa mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh sun kai hare-hare kan cibiyoyin bada wutan lantarki kimani 45 a cikin kasar Iraki a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.
Ma’aikatar wutan lantarki ta kasar Iraki ta bayyana cewa a makon da ya gabata mayakan Daesh sun wargaza cibiyar bada wutan lantarki na Lardan Sahahuddeen da makaman katusha, wanda ya haddasa katsewar wutan lantarki a lardin.
342/